Isa ga babban shafi
Rasha-Koriya

"Koriya ta Arewa na bukatar tsaro kan shirinta na Nukiliya"

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, Koriya ta Arewa na bukatar tabbacin samun tsaro daga kasashen duniya kafin ta kawo karshen shirinta na makaman Nukiliya.

Shugaban Koriya ta Arewa  Kim Jong-un da shugaban Rasha Vladimir Poutine a birnin Vladivostok
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un da shugaban Rasha Vladimir Poutine a birnin Vladivostok (Foto: Reuters)
Talla

Shugaba Vladimir Putin da ke magana jim kadan da kammala ganawarsa da Kim Jong-un a Vladivostok da ke can gabashin Rasha, ya ce, Koriya ta Arewa na bukatar tabbacin samun tsaro da kuma kare ‘yancinta muddin ana son ta kawo karshen shirinta a Nukiliya.

Putin ya ce, akwai bukatar sake karfafa dokokin kasa da kasa da za su rika fayyace makomar aukuwar lamurra a duniya, amma ba a rika karkata ga dokar wanda ya fi karfi ba.

Ana ganin dai Putin ya yi shagube ne ga Amurka saboda yadda take kokarin amfani da karfi kan Koriya ta Arewa.

Ganawar Putin da Kim Jong-un na zuwa ne bayan tabarbarewar tattaunawa tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa a cikin watan Fabairun da ya gabata, lokacin da Kim ya gana da Donald Trump a babban birnin Hanoi na kasar Vietnam.

Rahotanni sun ce, tattaunawar ta sukurkuce ne bayan Koriya ta Arewa ta bukaci janye mata takunkuman karayar tattalin arziki baki daya, kafin ta kwance damarar Nukiliyarta, bukatar da Amurka ta yi watsi da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.