Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu a harin Sri Lanka ya tasamma 300

Rahotanni daga kasar Sri Lanka na nuni da cewa adadin wadanda harin, bama-bamai a majami'u da Otel ya hallaka ya kai 290 baya ga wasu fiye da 500 da suka samu munanan raunuka.

Tuni dai kasashen duniya suka yi tir da harin na Sri Lanka
Tuni dai kasashen duniya suka yi tir da harin na Sri Lanka REUTERS
Talla

Bayanan baya-bayan nan da gwamnatin Sri Lanka ta fitar ya nuna cewa an samu rasuwar wasu daga cikin wadanda suka jikkata a harin wanda har bama-bamai 8 suka tashi ciki har da 2 na kunar bakin wake.

Yayin faruwar lamarin dai mutane 207 aka tabbatar da mutuwarsu a wasu majami'un kasar da Otel, dai dai lokacin da ake tsaka da shagulgulan Easter.

Tuni dai gwamnatin kasar ta bakin Firaminista Ranil Wickremesinghe ta sanar da kama wasu mutanen 8 da ake zargi da hannu wajen kai jerin hare haren.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.