Isa ga babban shafi
Isra'ila

Netanyahu ya kama hanyar sake lashe zaben Isra'ila karo na 5

Kafofin yada labaran Isra'ila sun sanar da cewar, Firaminista Benjamin Netanyahu ya kama hanyar lashe zaben kasar wanda zai bashi damar yin wa’adi na 5. Tuni Netanyahu da abokin karawar sa tsohon shugaban sojin kasar Benny Gantz suka bayyana samun nasara a zaben.

Firaminista Benyamin Netanyahu
Firaminista Benyamin Netanyahu REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Bayan kammala kidaya kashi 97 na kuri’un da aka kada, sakamakon zaben ya nuna cewar Jam’iyar Likud ta Firaminista Benjamin Netanyahu da kawayen ta sun samu tsakanin kujeru 65 daga cikin kujeru 120 dake Majalisar kasar, abinda zai basu damar samun nasara.

Ganin yadda zaben ya gudana da yadda ake tafiya kankankan tsakanin Netanyahu da babban mai adawa da shi Benny Gantz, an dan samu shakku da kuma fargaba lokacin da aka fara bayyana sakamakon, abinda ya sa Netanyahu da Gantz kowa ya fito ya bayyana samun nasara.

Firaminista Netanyahu ya bayyana sakamakon zaben a matsayin gagarumar nasara, inda yake cewa ya fara tattaunawa da jam’iyyun kawance kuma gwamnatin sa zata zama na ‘yan ra’ayin rikau ne zalla.

Shi kuwa Benny Gantz ya bayyana sakamakon a matsayin ranar tarihi, inda ya bukaci Netanyahu ya basu damar kafa gsabuwar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.