Isa ga babban shafi
Isra'ila

Zaben Isra'ila zai fayyace makomar Netanyahu

Al’ummar Isra’ila na gudanar da zaben gama-gari da ake kallo a matsayin mafi zafi a tarihin kasar, ganin irin kalubalen da Firaminista Benjamin Netanyahu wanda ke neman wa’adi na 5 ke fuskanta a zaben.

Benyamin Netanyahu na fuskantar kalubale musamman daga babban mai hamayya da shi wato, Benny Gantz
Benyamin Netanyahu na fuskantar kalubale musamman daga babban mai hamayya da shi wato, Benny Gantz REUTERS/Nir Elias
Talla

Zaben zai fayyace makomar Netanyahu da ake zargi da laifin cin hanci da rashawa, yayinda yake fuskantar barazanar rasa kujerasa daga babban mai hamayya da shi, wato Benny Gantz, tsohon hafsan sojin kasar.

Gantz na jam’iyyar Blue and White na kalubalantar Netanyahu na jam’iyyar Likud Party akan tabarbarewar tsaron kasar, yana mai alkawarin tabbatar da tsaftatacciyar siyasa.

Tun da misalin karfe 4 na safe agogon GMT aka bude rumfunan zabe, yayinda ake saran bayyana sakamako a ranar Laraba.

KADAN DAGA CIKIN TARIHIN ISRA'ILA

Ita dai Israila ta gwabza yake-yake da dama da makotanta Larabawa, abinda ya bata damar ci gaba da mamaye Gabar Yamma da Kogin Jordan, daya daga cikin wuraren da ke da matukar tasiri wajen kulla zaman lafiya da Falasdinawa.

Kasashen duniya na kallon Israila a matsayin kasa mafi karfi a Gabas ta Tsakiya, wadda ke dauke da makaman nukiliya, kuma a kowacce shekara tana karbar Dala biliyan 4 daga Amurka a matsayin agajin soji.

Ya zuwa yanzu, kasar ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ne kawai da kasashen Masar da Jordan a Yankin.

Adadin Yahudawan Isra'ila ya karu zuwa kusan miliyan 9 kamar yadda alkaluma suka nuna A bara, kuma a cikin 'yan shekarun da suka gabata, Isra'ila ta yi ta gina gidaje domin tsugunar da Yahudawa dubu 650 a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Birnin Kudus duk da adawar da kasashen duniya ke yi.

Isra'ila ta dada samun goyon baya daga Donald Trump a 'yan kwanakin nan, ganin yadda ya mallaka mata yankin Tuddan Golan da kuma ayyana birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatinta.

Isra'ila ta yi fice a harkar sadarwa, sannan tana da arzikin iskar gas da take fitarwa zuwa kasuwannin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.