Isa ga babban shafi
Tattalin Arziki

Akwai fargaba kan tattalin arzikin duniya a bana- IMF

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya bayyana fargaba kan hasashen koma baya da ya samu na tattalin arzikin duniya a watanni ukun wannan shekara.

Manajar asusun bada lamuni na duniya Christine Lagarde
Manajar asusun bada lamuni na duniya Christine Lagarde Reuters
Talla

Rahoton Hasashen Asusun na IMF ya bayyana manyan batutuwan da suka haifar da koma bayan da aka samu da suka hadar da matsalolin cinikayya da batun ficewar Birtaniya daga kungiyar Turai dama sauran muhimman dalilai.

A cewar asusun na IMF matukar ana fatan warwarewa matsalolin da suka haifarwa tattalin arzkin koma baya, dole ne a kawo karshen takaddamar cinikayya tsakanin Amurka da China.

Babban Jami'in da ke kula da tattalin arziki na IMF Gita Gopinath ya ce tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin duniya ya yi a watanni ukun farkon shekarar nan ya kai kashi 70 a cikin 100 matakin da ke nuna babban koma baya.

Rahoton asusun ya kuma nuna cewa kasashen da ke amfani da kudin Euro anan abin ya fi kamari, musamman kasar Jamus inda aka sami kashi 50 cikin dari na hasashen habakar tattalin arzikin da aka yi cikin shekarar nan, yayinda a kasar Italiya kuma tattalin arzikin a tsaya cik.

Ka zalika rahoton na IMF na nuna cewa takaddama kan shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai zai sanya kasar zamowa 'yar gaba gaba a jerin kasashen Turai da za su samu koma bayan tattalin arziki a bana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.