Isa ga babban shafi
Japan

An sake tsare tsohon shugaban Nissan a Japan

Hukumomin kasar Japan sun sake kama tsohon shugaban kamfanin hada motocin Nissan, Carlos Ghosn kan wasu zarge zargen amfani da kudade ta hanyoyin da basu kamata ba.

Carlos Ghosn Tsohon Shugaban kamfanin Nissan
Carlos Ghosn Tsohon Shugaban kamfanin Nissan Reuters
Talla

Jami’an tsaron jiya alhamis sun yi sammako zuwa gidan Ghosn dake Tokyo inda suka tsare shi kan abinda suka kira kwashe kudaden ajiyar kamfanin Dala miliyan 15 wanda suka ce Ghosn yayi amfani da Dala miliyan 5 daga cikin su.

Ghosn ta hannu wakilin sa yayi watsi da zargin inda yake cewa ba zai karya masa gwuiwa ba.

A zaman kotun na baya tsohon shugaban Kamfanin kera motoci na Nissan, Carlos Ghosn ya shaida wa wata kotu a birnin Tokyo na Japan cewa, an yi kuskuren zargin sa da kuma tsare shi kan badakalar cin hanci da rashawa a kamfanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.