Isa ga babban shafi
Brunei

Brunei ta fara aiki da zallar shari'ar Musulunci a kasar

Kasar Brunei ta kaddamar da dokokin shari’ar Musulunci da suka kunshi kashe duk wanda aka samu da laifin zina ko luwadi ta hanyar jifan sa da duwatsu, yayinda za a rika yanke hannun barawo da kuma yin bulala ga 'yan madigo.

Sultan Hasanal Bolkiah na Brunei
Sultan Hasanal Bolkiah na Brunei REUTERS/Ahim Rani/Files
Talla

Brunei da ke karkashin mulkin Sultan Hassanal Bolkiah ta fara aiki da dokokin na shari’ar Musuluncin gadan-gadan a ranar Laraba bayan tsaikon da aka samu na tsawon shekaru.

Har ila yau dokokin sun kunshi hukuncin kisa kan 'yan fashi da makami da kuma masu yi wa mata fyade.

Kazalika za a yi wa duk matar da aka samu da laifin tarawa da mace ‘yar uwarta bulala 40 ko kuma daurin shekaru 10 a gidan yari.

Wasu sassan na dokokin, za su rika shafar hatta wadanda ba Musulmai ba, kamar mutumin da aka samu da laifin furta kalaman da ba su dace ba ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

A wani jawabi da ya gabatar ga al’ummar kasar ta kafar talabijin, Sultan Bolkiah ya kuma bukaci a bada kaimi wajen koyar da ilimin addinin Islama.

Sai dai tuni aka fara samun martani daga sassa daban daban na duniya, in da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana dokokin a matsayin zalunci da rashin tausayi, yayinda fitattun taurarin duniya karkashin jagorancin jarumin fina-finan nan, George Clooney da mawakin nan Elton John suka bukaci a kaurace wa otel-otel din da kasar ta Brunei ta mallaka a kasashen ketare kamar a Amurka da Turai.

Kungiyar Tarayyar Turai da ‘yan siyasa har ma da kungiyoyin kare hakkin dan Adam duk sun caccaki matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.