Isa ga babban shafi
Birtaniya

Majalisar Birtaniya na kada kuri'a kan Brexit

‘Yan Majalisar Dokokin Birtaniya na shirin kada wata sabuwar kuri’a a yau Laraba da zummar samar da mafita dangane da kiki-kakar yarjejeniyar ficewar kasar daga gungun kasashen Turai.

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May HO / AFP / PRU
Talla

Kimanin shekaru uku kenan da Birtaniya ta tsayar da shawarar raga gari da Kungiyar Kasashen Turai, amma ‘yan Majalisar kasar sun gaza cimma matsaya guda kan yadda za aiwatar da tsarin ficewar, in da ma wasu daga cikinsu ke tunanin kodai ma a jingine batun ficewar ne baki daya.

A halin yanzu dai, an gabatar da gyare-gyare da dama kan tsarin ficewar, yayinda shugaban Majalisar Dokokin, John Bercow zai fara zabar daya daga cikin gyare-gyaren da yake ganin zai kai su ga gaci.

Wasu daga cikin mambobin Majalisar kuwa, na da ra’ayin sake hambarar da yarjejeniyar da Firaminsta Theresa May ta gabatar, wasu kuma, na da ra’ayin ficewa daga Turai ba tare da wata yarjejeniya ba, ko kuma ma dai, a dakatar da shirin ficewar.

A can baya dai, Majalisar Dokokin ta yi watsi da tsarin da Firaminista May ta gabatar har sau biyu duk da cewa ta shafe watanni 17 tana tattaunawa da mahukuntan Brussels kan yarjejeniyar.

Muddin Majalisar ta sake watsi da yarjejeniyar a wannan karo, babu shakka hakan zai sanyaya guiwar Firaministar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.