Isa ga babban shafi
Venezuela

Guaidó ya bukaci fita sabuwar zanga-zanga a Venezuela

Jagoran ‘yan adawar Venezuela, Juan Guaido ya bukaci gudanar da gagarumar zanga-zanga a sassan kasar, yayin da ya sanar da shirinsa na komawa gida bayan shafe mako guda yana ziyarar ganawa da kasashen da ke mara masa baya a yankin Latin Amurka.

Jagoran adawar Venezuela da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa Juan Guido
Jagoran adawar Venezuela da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa Juan Guido REUTERS/Daniel Tapia
Talla

A wani sako da ya aike ta shafinsa na Twitter, Juan Gaudo da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar Venezuela ya ce, yana kira ga daukacin al’ummar kasar da su yi gangami a yau Litinin da misalin karfe 11 na safe, agogon kasar.

Sai dai Guaido wanda ya samu goyon bayan kasashen duniya fiye da 50 a ikirarinsa na shugaban rikon kwarya, bai yi cikakken bayani kan ranar da zai koma gida ba.

Guaido dai ya yi watsi da haramcin tafiye-tafiye da shugaban kasar Nicolas Maduro ya dora masa, in da ya silale ta kan iyakar kasar zuwa Colombia a makon jiya da zummar shigo da kayan agaji cikin kasar da kuma ganawa da mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence da ya ziyarci Colombia.

Kazalika, Guaido mai shekaru 35 ya wuce can Brazil , in da ya gana da shugaban kasar, Jair Bolsonaro, kafin a ranar Jumma’ar da ta gabata ya isa Paraguay da Argentina, har ma da Ecuador, in da ya yi hutun karshen mako.

Dambarwar siyasar Venezuela na dada kamari ne a daidai lokacin da al’ummar kasar ke cikin tsaka mai wuya, inda rahotannin baya-bayan nan ke cewa, jama’a na shan bakar wahala wajen samun tsaftataccen ruwan sha.

Mutane da dama ne ke layi a birnin Caracas domin cika gorarsu da ruwan da ke kwaranyowa daga tsauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.