Isa ga babban shafi
China-Korea

China ta bukaci sassauta wa Korea ta Arewa takunkumai

China ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya tattauna kan batun sassauta takunkuman da aka kakaba wa Korea ta Arewa bayan shugaba Donald Trump da Kim Jong-un sun gaza cimma matsaya a taron da suka gudanar a Hanoi.

China ta bukaci sassauta takunkuman Korea ta Arewa bayan shugaba Donald Trump da shugaba Kim Jong-un sun yi baran-baran a taronsu na birnin Hanoi
China ta bukaci sassauta takunkuman Korea ta Arewa bayan shugaba Donald Trump da shugaba Kim Jong-un sun yi baran-baran a taronsu na birnin Hanoi REUTERS/Leah Millis
Talla

Kasar China ta kasance babbar aminiyar kasuwancin Korea ta Arewa kuma kawarta ta kut da kut, amma ta goyi bayan kudirin Majalisar Dinkin Duniya na sanya wa kasar takunkumi bayan gwamnatin Kim Jong-un ta yi ta gwaje-gwajen makaman nukiliya da masu linzami a ‘yan shekarun baya-bayan nan.

A yanzu dai, wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta fitar ta ce, Kasashen Korea ta Arewa da Amurka sun fahimci cewa, dage takunkuman a yanzu nada muhimmanci dangane da shirin kwance nukiliyar Korea ta Arewar.

China ta ce, akwai bukatar aiwatar da dage takunkumin da kuma kwance nukiliyar a lokaci guda, yayinda ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya fara tattaunawa domin sake nazari kan batun takunkuman.

A jiya Alhamis ne, shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Korea ta Arewa, Kim Jong-un suka kammala taronsu na birnin Hanoi ba tare da cimma jituwa ba, in da suka samu banbancin ra’ayi kan dage wa Koriyar takunkuman.

Trump ya ce, Kim ya bukaci a janye dukkanin takunkuman amma gwamnatin Koriyar ta musanta haka, tana mai cewa, wani bangare na takunkuman ta bukaci a janye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.