Isa ga babban shafi
Venezuela

Juan Guaido ya bayyana fatan sa na komawa gida,Venezuela

Shugaban yan adawan Venezuela Juan Guaido yace ko ana ha maza ha mata sai ya koma gida duk da hadarin da hake ke tattare da shi.Guaido wanda ya ziyarci Colombia wajen taron wakilan kasashen Lima dake yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Maduri yace zaman sa a waje ba zai taimakawa kasar ba, saboda haka zai koma gida.

Juan Gaido dan adawa da gwamnatin Nicolas Maduro
Juan Gaido dan adawa da gwamnatin Nicolas Maduro REUTERS/Manaure Quinter
Talla

Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya shaida masa cewar shugaba Donald Trump na bayan sa dari bisa dari, yayin da Ministan harkokin wajen Colombia Carlos Holmes Trujillo yace muddin gwamnatin Maduro ta dauki mataki a kan Guaido ko iyalan sa to zasu mayar da martini mai karfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.