Isa ga babban shafi
VENEZUELA

Guaido zai yi yakin shigo da abinci a Venezuela

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya bayar da umarnin rufe iyakar kasar da Brazil, a daidai lokacin da jagoran ‘yan adawa, Juan Guaido ke shirin jagorantar aikin shigar da kayayyakin jinkai a cikin kasar. Har ila yau Maduro ya ce, yana tunanin daukar irin wannan mataki a kan iyakar kasar da Colombia.

Jagoran 'yan adawar Venezuela,  Juan Guaido
Jagoran 'yan adawar Venezuela, Juan Guaido REUTERS/Manaure Quintero
Talla

Guaido wanda ke samun goyon bayan kasashen duniya fiye da 50 ya ce, shi da kansa ne zai jagoranci ayarin motocin da ke dauke da kayayyakin agaji da suka makale da ke bangaren Colombia domin shigar da su a cikin kasar ta Venezuela.

Tun a jiya Alhamis ne Guaido mai shekaru 35 a duniya ya bar birnin Caracas don kaddamar da wannan aiki da gwamnatin Muduro ta ce, ba z ta bayar da damar gudanar da shi ba saboda a cewarsa Amurka na shirya yin amfani da sojoji ne don mamaye kasar.

Ko baya ga Guaido, akwai wasu ‘yan majalisar dokoki daga bangaren adawa da suka bar birnin na Caracas cikin ayarin motoci zuwa kan iyakar kasar don fara aikin raba wadannan kayayyakin agajin da suka share kusan makonni uku makale a bangaren kasar Colombia.

Daya daga cikinsu mai suna Yenet Fermin, ya ce tabbas Maduro zai yi kokarin yin amfani da jami’an tsaro domin kange iyakar, amma ba wanda zai hana soma raba wa jama’a wadannan kayayyaki a wannan karo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.