Isa ga babban shafi
VENEZUELA

Trump ya bai wa sojojin Venezuela zabi

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce sojojin kasar Venezuela na da zabi, ko dai su goyi bayan jagoran ‘yan adawa Juan Guaido ko kuma su rasa samun afuwa, yana mai cewa abu ne mai yiyuwa Amurka ta yi amfani da kowacce dama a kan kasar.

Shugaban Nicolas Maduro na samun goyon bayan sojin kasar
Shugaban Nicolas Maduro na samun goyon bayan sojin kasar Miraflores Palace/Handout via REUTERS
Talla

Trump wanda ke jawabi a gaban magoya bayansa da kuma ‘yan asalin kasar Venezuela mazauna birnin Miami, ya ce wadanda suka goyi bayan Guaido za a yi musu afuwa domin ci gaba da rayuwa tare da iyalansu, wadanda suka ki kuwa za su yi da na sani.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin shugaban kasar, Nicola Maduro ta hana shigo da kayayyakin agaji daga Amurka domin taimaka wa al’ummar kasar da ke cikin matsananciyar bukatar abinci.

Mr. Guaido ya gargadi gwamnatin Maduro da ta bayar da hanyar shigo da kayayyakin agajin nan da ranar Asabar mai zuwa.

Mr. Guaido na ci gaba da kallon kansa a matsayin shugaban kasar Venezuela na riko, yayin da kimanin kasashen duniya 50 ke mara masa baya har sai Maduro ya amince da sake gudanar da sabon zaben shugaban kasa, matakin da ya yi watsi da shi duk da gargadin da kasashen suka yi masa, abin da ya dada dagula rikicin siyasar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.