Isa ga babban shafi
Save the Children

Yaki na kashe jarirai dubu 100 a kowacce shekara

Jarirai sama da dubu 100 ne ke mutuwa a shekara, sakamakon yake-yake da sauran tashe-tashen hankulan da ake fama da su a sassan duniya kamar dai yadda wani rahoton Kungiyar Save The Children ya nuna.

Tashe-tashen hankula na kashe jarirai sama da dubu 100 a kowacce shekara
Tashe-tashen hankula na kashe jarirai sama da dubu 100 a kowacce shekara Action4Alfie / AFP
Talla

Rahaton wanda aka fitar a ranar Juma’a a kasar Jamus, ya ce, kimanin jarirai dubu 550 ne suka rasa rayukansu tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017 a kasashe 10 da ke fama da yaki da suka hada da Afghanistan da Yemen da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Congo da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Syria da Iraqi da Mali da Najeriya da kuma Somalia.

Tashe-tashen hankulan sun jefa kananan yara cikin bala’in yunwa, yayin da kuma suka rasa samun agajin magunguna da abinci.

Save The Children ta ce, wannan matsalar ta kashe kananan yaran ta ta’azzara da ninki uku idan aka kwatanta da shekaru 20 da suka gabata, tana mai cewa, binciken da ta gudanar a shekarar 2017, ya nuna cewa, kimanin kananan yara miliyan 420 ne ke rayuwa a wurare masu fama da rikici a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.