Isa ga babban shafi
Iran- Amurka

Iran ta soki Amurka kan yi mata zagon-kasa

Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya caccaki Amurka kan zagon-kasar da take yi wa kasar a yayin da dubban Iraniyawa ke bikin cika shekaru 40 da juyin juya halin kasar.

Shugaban Iran Hassan Rohani na jawabi a gaban dandazon Iraniyawa a dandalin Azadi
Shugaban Iran Hassan Rohani na jawabi a gaban dandazon Iraniyawa a dandalin Azadi Hossein Zohrevand/Tasnim News Agency/via REUTERS
Talla

Shugaba Rouhani ya shaida wa dandazon Iraniyawa a dandalin Azadi da ke birnin Tehran cewa, makiyan kasar ba za su cimma mummunar manufarsu akan kasar ba, musamman ma idan aka yi la’akari da dimbin jama’ar da suka yi fitan dango a kan titunan kasar.

Mata da ‘yan tawaye sanye da kakin soji da sauran fararen hula sun yi maci a birnin na Tehran duk da ruwan saman da ake tafkawa domin tunawa da wannan rana ta 11 ga watan Fabairun shekarar 1979, lokacin da Ayatollah Ruhollah Khomeini ya kawo karshen mulkin mulaka’un gidan sarauta.

A yayin gudanar da bikin na yau, an jera wasu na’ukan manyan makamai masu Linzami da Iran ta kera, a wani mataki na nuna turjiya kan takunkuman da Amurka ta kakawa kasar jim kadan da janyewarta daga yarjejeniyar nukiliyar da Iran din ta cimma da manyan kasashen duniya, yarjejniyar da shugaba Donald Trump ya bayyana a matsayin shiririta.

Kazalika an gabatar da wani shirye-shiryen kudiri a bainal jama’a da ke bayyana irin biyayyar da Iraniyawa ke yi wa jagoran addinin kasar, Ayatolla Ali Khameinei, yayin da a gefe guda kudirin ya bayyana Trump a matsayin sakarai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.