Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Rasha za ta kera wani nau'in makami mai linzami nan da 2020

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya ce kasar za ta gina wani sabon makami mai linzami nan da shekaru biyu masu zuwa, bayan ficewa daga yarjejeniyar kerar makaman da ta yi tare da kasar Amurka.

Wani nau'in makamin nukiliya mallakin kasar Rasha
Wani nau'in makamin nukiliya mallakin kasar Rasha (Photo : Reuters)
Talla

Ministan ya shaidawa jami’an ma’aikatan tsaron kasar cewar, tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020 za su kera wani makamin mai linzami na kasa, da zai yi aiki har a cikin ruwa, mai cin dogon zango saboda nasarar amfani da shi da aka samu a Syria.

Shoigu ya ce a cikin wanna lokaci kuma za su kera wani sabon makami mai linzami da ke cin dogon zango domin biyan bukatun kasar.

Masana harkokin tsaro sun ce ficewa daga yarjejeniyar kera makaman da aka kula tsakanin Rasha da Amurka a shekarar 1987 zai bude kofar kera sabbin makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.