Isa ga babban shafi
Cancer-Lafiya

Mutane masu kiba na cikin hadarin kamuwa da cutar Cancer - Bincike

Masana a fannin lafiya na ci gaba da gargadi kan yadda muguwar kiba da aka fi sani da Obesity ke matsayin babbar silar haddasa cutar Cancer ko kuma daji, cutar da masanan ke cewa yanzu tafi tsananta tsakanin matasan da shekarunsu ke kasa da 50.

Kwayar halittar cutar Cancer wadda aka fi sani da daji
Kwayar halittar cutar Cancer wadda aka fi sani da daji Juan Gaertner/Shutterstock.com
Talla

A wani gwaji da masana a bangaren lafiya suka yi kan kashi biyu cikin 3 na al’ummar kasar Amurka ya nuna cewa rabin mutanen da suka kamu da cutar ta Cancer na da nasaba da mummunar kibar da suke da ita, wanda kuma bayanan masanan ke cewa cutar ta tsananta ne daga 1995 zuwa 2015.

Ka zalika rahoton da msanan suka fitar ya nuna cewa cutar ta fi saurin hauhawa a jikin matasa fiye da mutane masu yawan shekaru, inda ya ce hadarin cutar na karuwa da akalla kashi 1 duk shekara a jikin mutanen da shekarunsu ya fara daga 45 zuwa 49 sai dai kuma hadarinta na rubanya a jikin masu shekaru 30 zuwa 34.

Rahoton ya kuma bayyana cewa cutar tafi muni a jikin matasan da ke da shekaru 25 zuwa 29 inda a duk shekara ta ke hauhawa da akalla kashi 4 da digo 4.

Cutar ta Cancer wadda ke cikin jerin cutuka masu hadari kuma su ke da saurin kisa wadda kuma tafi tsananta jikin mutanen masu mummunar kiba kana kuma matasa, kai tsaye ta na taba koda baya ga haddasa cutar hanta kana ta taba mahaifa ga mata, a wasu lokutan ma ta kai ga taba ‘ya’yan hanjin cikin dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.