Isa ga babban shafi
Tattalin Arziki-Davos

Taron tattalin arziki na birnin Davos zai daidaita rikicin kasuwanci

Kasashe 75 da ke halartar taron kasuwanci na duniya a birnin Davos na Switzerland, sun fara tattaunawa kan samar da wasu sabbin dokokin kasuwancin kasa da kasa.Sabbin dokokin da ake shirin samarwa dai za su shafi hada-hadar kasuwanci ta shafukan Intanet ne tsakanin kasashen duniyar.

Taron wanda Amurka da Birtaniya suka kauracewa ya sha alwashin magance mafi akasarin korafe-korafen da kasashe ke yi a huldar kasuwanci.
Taron wanda Amurka da Birtaniya suka kauracewa ya sha alwashin magance mafi akasarin korafe-korafen da kasashe ke yi a huldar kasuwanci. REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Babbar jami’ar lura da sashen kasuwancin kungiyar kasashen Turai EU, Cecilia Malmstrom ce ta bayyana fara kokarin cimma yarjejeniyar tsakanin kasashen 75, wadanda ta ce sun hada da Amurka da China, mafiya karfin tattalin arziki, a tsakanin takwarorinsu na duniya.

Tattaunawar samar da dokoki kan kasuwancin shafukan Intanet a karkashin jagorancin hukumar sasanta rikicin kasuwanci ta duniya WTO, na zuwa yayinda aka shafe tsawon watanni ana kokarin kawo karshen yakin kasuwancin da ya barke tsakanin Amurka da China.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sha zargin hukumar sasanta rikicin kasuwancin ta Duniya, da sassauta wasu dokokin kasa da kasa domin bai wa China fifiko kan Amurkan a fagen kasuwanci.

Sai dai babbar jami’ar kungiyar EU Ccecilia Malmstrom ta ce za’a kawo karshen mafi akasarin korafe korafen kan alakar kasuwanci tsakanin kasashe, da zarar an samar da sabbin dokokin da za su tabbatar da kyakkyawan yanayi na kasuwanci tsakanin kasashe a shafukan intanet.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.