Isa ga babban shafi
Duniya

Wasu Shugabanin kasashe sun kauracewa taron Davos

Wakilan kasashe da na kamfanoni sama da dubu uku ne ke halartar taron tattalin arziki na Birnin Davos da aka soma a jiya talata, to sai dai taron na bana bai samu halartar wasu shugabannin kasashen duniya ba.

Zauren taron Tattalin arziki na Davos
Zauren taron Tattalin arziki na Davos REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Shugaban Amurka Donald Trump, ba ya cikin mahalarta taron sakamakon rikicinsa da bangaren majalisa, yayin da takwanransa na Faransa Emmanuel Macron ya kaurace wa taron sakamakon matsaloli masu nasaba da tattalin arziki a cikin gida, sai kuma Firamiinistar Birtaniya Theresa May da ita ma ba za ta halarci taron ba, a daidai lokacin da take kokarin shawo kan ‘yan siyasar kasar game da yarjejeniyar ficewar daga gungun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.