Isa ga babban shafi
Duniya

Ayyukan ta'addanci a Tekunan duniya sun tsananta a bana - Rahoto

Rahoton wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa, an fuskanci karuwar aikata laifukan fashi da makami, hadi da yin garkuwa da mutane a tekunan duniya.

Rahotan ya nuna cewa a karshen shekarar bara, sau 41 ana yi wa jiragen ruwa fashi tare da garkuwa da ma'aikatansu a gabar tekun Najeriya.
Rahotan ya nuna cewa a karshen shekarar bara, sau 41 ana yi wa jiragen ruwa fashi tare da garkuwa da ma'aikatansu a gabar tekun Najeriya. PASCAL POCHARD-CASABIANCA / AFP
Talla

Binciken ya kuma alakanta hakan, da karuwar aikata manyan laifukan a gabar tekun yammacin Afrika.

A cewar hukumar ta IMB mai hedikwata a Malaysia, a shekarar 2018 an yi wa manyan jiragen ruwa fashi da kuma garkuwa da mutane sau 201 a tekunan duniya, fiye da na shekarar 2017 da aka samu rahoton aikata laifukan sau 180.

Rahoton ya ce a karshen shekarar 2018, gabar tekun yammacin Afrika ya fi fuskantar wannan matsala ta ‘yan fashin teku, la’akari da cewa a karshen shekarar ta bara, sau 41 aka yiwa jiragen ruwa fashi hadi da yin garkuwa da ma’aikatansu a gabar tekun Najeriya kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.