Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnati za ta yi muhawara da Faransawa masu bore

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da shirin gudanar da mahawarar kasa wadda za ta bai wa 'yan kasar damar bayyana ra’ayoyinsu domin kawo karshen zanga-zangar da aka kwashe kusan watanni biyu ana gudanarwa a kasar.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa Michel Euler/Pool via REUTERS
Talla

A cikin wata wasika da ya aika wa al'ummar kasar, shugaba Macron ya ce, mahawarar za ta bada damar yin tambayoyi kusan 35 kan batutuwan da suka shafi haraji da dimokiradiya da muhalli da shige da fice.

Shugaban ya ce, matsayin jama’a zai bada damar kulla wata sabuwar yarjejeniyar kasa da kuma shirya ayyukan gwamnati da na 'yan majalisu, kana da matsayin Faransa a kungiyar Turai da kuma siyasar duniya.

Macron ya bada misalin tambayoyin mahawarar kamar haka, wane haraji kuke so a rage? Kuna bukatar majalisa ta shata adadin bakin da ake bukata su shiga Faransa?

A bangare guda, Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Duniya Reporters Without Borders da kuma kafafen yada labaran Faransa, sun bayyana bacin rai kan yadda wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar suke kai musu farmaki.

Koken kafafen yada labaran na zuwa ne bayan  masu zanga-zangar sun far wa 'yan jaridu da ke bada rahoto kan halin da ake ciki a ranar Asabar, in da har ma suka fasa hancin jami'in tsaron da ke bai wa 'yan jaridun kariya.

Karo na tara kenan da masu sanye da riguna launin dorawa ke gudanar da zanga-zangar a duk karshen mako, wadda ta samo asali bayan karin farashin albarkatun mai da kuma wasu sauye-sauyen tattalin arziki da shugaba Macron ya gabatar a watan Nuwamban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.