Isa ga babban shafi
Bakin haure

Fafaroma ya bukaci Turai ta agaza wa bakin teku

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis ya bukaci shugabannin Kasashen Turai da su nuna kwakkwaran goyon baya ga ‘yan gudun hijira 49 da ke walagigi a cikin jiragen ruwa a gabar tekun Malta bayan wasu kasashe sun hana su tashar tsayawa.

Shugaban Darikar Katolika ta duniya, Fafaroma Francis
Shugaban Darikar Katolika ta duniya, Fafaroma Francis REUTERS/Max Rossi
Talla

A yayin da Fafaroma ya yi wannan kira a karshen mako, kasashen Italiya da Malta sun jaddada matsayarsu ta hana wadannan jirage biyu dauke da bakin hauren tashar tsayawa.

Fafaroman ya shaida wa dubban jama’a a dandalin Saint Peters cewa, bakin hauren 49 sun shafe kwanaki masu yawa a tekun Mediteranean kuma a cikin jiragen mallakin kungiyoyin agaji, in da suke neman tudun-mun-tsira.

Fafaroman ya ce, yana matukar bukatar kasashen na Turai da su hada kai wajen agaza wa wadanan bayin-aall.

A farkon makon jiya ne, ita ma hukumar Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci mambobin kasashen nahiyar da su karbi bakin hauren da ke cikin mawuyacin hali.

Ba a karon farko kenan ba da Fafaroma Francis dan asalin Argentina ke rokon shugabannin kasashen Turai da su bude kan iyakokinsu, amma babu wata alama kan cewa, Italiya za ta sauya matsayarta ta hana bakin mafaka.

Ministan Cikin Italiya mai ra’ayin rikau, Matteo Salvini y ace, a yanzu babu wasu ‘yan gudun hijira da ke kwarara cikin kasar, tare da fadin cewa, babu wani abu da zai sauya tsarinsu.

Ministan ya kuma jaddada cewa, kan iyakokin kasar ta Italiya za su ci gaba da kasancewa a rufe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.