Isa ga babban shafi
Amurka-China

Amurka da China na ganawa don warware rikicin kasuwancinsu

Wakilan kasashen Amurka da na China, sun gana kai tsaye yau Litinin a birnin Beijing, dangane da yakin kasuwancin da ya kullu a tsakaninsu.Ganawar dai, ita ce ta farko bayan da a karshen shekarar bara, shugabannin kasashen biyu, suka amince da shirin warware rikicin kasuwancin da ya barke a tsakaninsu ta hanyar fara sassauta shi.

Rikicin dai ya haddasa kasashen biyu asarar miliyoyin kudi matakin da ya sanya hukumar kula da kasuwanci ta duniya shiga tsakani don sasantawa.
Rikicin dai ya haddasa kasashen biyu asarar miliyoyin kudi matakin da ya sanya hukumar kula da kasuwanci ta duniya shiga tsakani don sasantawa. 路透社
Talla

Tawagar wakilan Amurka ta halarci ganawar ta Yau ce a karkashin jagorancin Jeffery Gerrish, wanda bayan fitowa daga taron, yaki yi wa manema labarai karin bayani kan yadda tattaunawar ta gudana da matsayar da aka cimma, sai dai ya ce, wakilan na Amurka da China za su ci gaba da ganawa a gobe Talata.

Sai dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Lu Kang ya shaidawa manema labarai cewa bangarorin biyu suna da kwakkwarar aniyar warware yakin kasuwancin da ke tsakani.

Tawagar ta Amurkan da ta yi tattaki zuwa birnin na Beijing sun kunshi jami’ai daga ma’aikatun kasar na kasuwanci, ayyukan noma, da kuma makamashi.

An dai shafe watanni Amurka da China na rikici a fagen kasuwanci, lamarin da ya sa manyan kasashen duniyar kakabawa kayayyakin da su ke kai wa junansu haraji na sama da dala biliyan 300.

Ganawar ta yau ta zo ne wata guda, bayan da shugaban Amurka Donald Trump da Xi Jing-Pin na China suka cimma yarjejeniyar dakatar da matakan kakabawa kayayyakin da su ke musaya karin haraji, domin bai wa wakilansu damar tattaunawa don warware rikicin da ya kullu tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.