Isa ga babban shafi
Syria

Sabon fada ya barke a Syria

Fada ya barke a yammacin Aleppo tsakanin ‘yan tawaye da kuma mayakan sa-kai da ke samun goyon bayan kasar Turkiyya, a halin yanzu ya yadu zuwa lardunan Idlib da kuma Hama da ke kasar Syria.

Sojojin Turkiya a yankin Manbij
Sojojin Turkiya a yankin Manbij 路透社。
Talla

Kungiyoyin mayakan sa-kai 12 da ke samun goyon bayan Turkiyya, sun bukaci karin dakaru bayan share tsawon kwanaki biyu suna gwabza fada da mayakan da ke ikirarin jihadi a garuruwan Saraqeb, Ma’aret da kuma Al-Nohman.

A karshen shekara ta 2018 ne dakarun gwamnatin Syria suka shiga birnin Manbij a karon farko cikin shekaru shida biyo bayan barazanar hari da birnin ke fuskanta daga Turkiya.

Mayakan Kurdawa da ke rike da birnin na Manbij sun janye, tare da gayyatar dakarun gwamnatin Syria domin kula da shi saboda farbagar cewa, sojin Turkiya za su iya kaddamar da sabon farmaki kan birnin.

Turkiya na kallon Kurdawan YPG da ke samun goyon bayan Amurka a matsayin ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.