Isa ga babban shafi
China-Taiwan

Dole ne Taiwan ta dawo karkashinmu- China

Shugaban China Xi Jinping ya yi barazanar amfani da karfin soji don tabbatar da hadewar kasarsa da tsibirin Taiwan da ya balle tun bayan kawo karshen yakin basasar shekarar 1949.

Shugaba Xi Jinping na China
Shugaba Xi Jinping na China REUTERS/Mark Schiefelbein/Pool
Talla

Shugaba Xi Jinping ya ce, babu makawa hadewar China da Taiwan, in da ya gargadi cewa, duk wani yunkurin yayata ‘yancin cin gashin kan yankin, ba komai zai hadasa ba, face fito-na-fito.

Kalaman shugaba Xi sun harzuka takwararsa ta Taiwan, Tsai Ing-Wen wadda ta ce, al’ummar kasarta ba za ta amince da irin keta hakkokin demokradiyar da ake yi a lardin China ba.

Har yanzu dai, China na kallon Demokradiyar Taiwan a matsayin yankinta da ke fatan sake hadewa da shi duk da cewa, tun shekarar 1949, wato bayan kawo karshen yakin basasa, bangarorin biyu ke mulkin cin gashin kai.

Sai dai a yayin gabatar da jawabin cika shekaru 40 da China ta aika sakon lalama ga Taiwan domin ganin ta amince da batun hadewar da kuma kawo karshen fito-na-fito tsakanin sojojin kasashen biyu, shugaba Xi ya hakikance cewa, dole ne fa, a yanzu Taiwan ta amince da wannan bukata a wannan sabon zamani da muke ciki.

Koda dai, shugaban ya bayyana cewa, bangarorin biyu za su dunkule a matsayin kasa guda, amma masu mabanbantan tsare-tsare.

Taiwan na kallon kanta a matasyin kasa mai cikakken ‘yanci, in da take da takardar kudinta daban da kuma tsare-tseren siyasa da na shari’a, amma duk da haka China ba ta amince mata a matsayin ‘yantanciyar kasa a hukumance ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.