Isa ga babban shafi
Syria

Sojin Syria sun shiga Manbij don kare Kurdawa

Dakarun Gwamnatin Syria sun shiga birnin Manbij a karon farko cikin shekaru shida biyo bayan barazanar hari da birnin ke fuskanta daga Turkiya. 

Sojin Syria sun shiga Manbij ne bayan aniyar Amurka ta janye dakarunta daga Syria
Sojin Syria sun shiga Manbij ne bayan aniyar Amurka ta janye dakarunta daga Syria Courtesy Zoe Garbarino/U.S. Army/Handout via REUTERS
Talla

Mayakan Kurdawa da ke rike da birnin na Manbij sun janye, tare da gayyatar dakarun gwamnatin Syria domin kula da shi saboda farbagar cewa, sojin Turkiya za su iya kaddamar da sabon farmaki kan birnin.

Turkiya na kallon Kuradawan YPG da ke samun goyon bayan Amurka a matsayin ‘yan ta’adda.

A yanzu dai mayakan na bukatar agajin dakarun Syria ne bayan shugaba Donald Trump ya sanar da aniyasra ta janye dakarun Amurka dubu 2 a Syria, in da ya yi ikirarin cewa, an ci galabar mayakan ISIS da ke tayar da kayar baya don haka dakarunsu za su koma gida.

Sai dai manyan aminan Amurka sun musanta ikirarin na Trump domin a cewarsu, har yanzu akwai sauran rina a kaba kuma ficewar dakarun za ta maido da karsashin kungiyar ISIS.

Ita ma kungiyar Kurdawan na kallon matakin na Trump a matsayin yaudara, yayin da a yanzu Turkiya ta zafafa aikin sojinta a kusa da wuraren da Kurdawan ke kula da su tun bayan sanarwar ta Trump.

A bangare guda, Turkiyar ta ce, mayakan na Kurduwa da ke dauke da makamai ba su da hurumun neman agajin gwamnatin Syria game da ba su kariya daga hare-harenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.