Isa ga babban shafi
Dumamar yanayi-Duniya

Dumamar yanayi ta haddasa asarar fiye da dala biliyan 30 a duniya-rahoto

Wani rahoto da kungiyar agaji ta Christian Aid mai rajin kare muhalli ta fitar ya nuna yadda matsalar dumamar yanayi a shekarar 2018 ta haddasa asarar fiye dala biliyan 30 a sassa daban-daban na duniya.Cikin rahoton, kungiyar ta yi ikirarin cewa galibin dumamar yanayin da ke faruwa a nahiyar Turai jama’ar yankin ke assasata.

Rahoton ya ce sauyawar yanayi a Birtaniya kadai dumamarsa ta ninka zuwa kashi 30.
Rahoton ya ce sauyawar yanayi a Birtaniya kadai dumamarsa ta ninka zuwa kashi 30. @time
Talla

Rahoton wanda kungiyar Christain Aid ta fitar a yau, ya ce akwai bala’o’I 10 da aka fuskanta cikin shekarar nan wanda kowannensu ya lakume fiye da dala biliyan guda baya ga wasu hudu na daban mafi muni da kowannensu ya haddasa asarar fiye da dala biliyan 7, dukkaninsu sanadiyyar dumamar yanayi wadda rahoton ke cewa yanzu haka ta na ci gaba da ta’azzara, yayinda ta ke shirin kai wani mataki da dakile ta zai yi wahala.

A cewar rahoton, galibin bala’o’in na shekarar nan na da alaka da dumamar yanayi wanda ke faruwa sanadiyyar sauyin da ake haifarwa yanayin sakamakon sinadaran da masana’antu ke fitarwa ciki har da annobar guguwar Florence da Michael da aka yi ta fuskanta wanda su kadai suka haddasa asarar dala biliyan 17.

Rahotan ya gwada misali da ambaliyar ruwan Japan da ta hallaka mutane 230 baya ga lakume fiye da dala biliyan 7 wadda kuma ita ce mafi muni da kasar ta taba fuskanta cikin shekaru 25.

Rahoton ya ce sauyawar yanayi a Birtaniya kadai dumamarsa ta ninka zuwa kashi 30 akan na shekarun baya sanadiyyar zafin da gurbatacciyar iskar masana’antu.

Daraktan binciken na kungiyar Christian Aid Dr Kat Kramer ya ce duk da masana kimiyya sun gaza mayar da hankali kan juya tunanin duniya game da illar da masana’antu ke haifarwa ga yanayi, amma sun yi amanna cewa wutar daji, guguwa ko kuma jinkirin zuwan damina da tsawaitar rani na da alaka da yawaitar sinadaran da kamfanoni da masana’antu ke fitarwa musamman daga kasashe masu ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.