Alhaji Sulaiman Garba Krako Saminaka kan matakin Amurka na neman kasashe su rika biyanta kafin basu tsaro
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da aniyar kasar ta kawo karshen rawar da ta ke takawa a matsayin ‘yan sandar duniya, in da ya ke cewa, akwai bukatar kasashe su biya kudade kafin Amurkan ta ba su tsaro.
Trump ya bayyana haka ne a yayin ziyarar ba-zata da ya kai wa dakarun Amurka da ke Iraqi, kuma ya bayar da tabbacin cewa, ba zai janye dakarun ba kamar yadda ya yi a Syria. Sai dai tuni masharhanta kan al’amuran siyasa suka alakanta ziyarar Trump da wani yunkurin wanke kanshi daga caccakar da ake yi masa a ciki da wajen kasar, kamar yadda za ku ji karin bayani a hirar da Abdurrahman Gambo ya yi da Alh. Sulaiman Garba Krako Saminaka da ke fashin bakin siyasa a Amurka.