Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Alhaji Sulaiman Garba Krako Saminaka kan matakin Amurka na neman kasashe su rika biyanta kafin basu tsaro

Wallafawa ranar:

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da aniyar kasar ta kawo karshen rawar da ta ke takawa a matsayin ‘yan sandar duniya, in da ya ke cewa, akwai bukatar kasashe su biya kudade kafin Amurkan ta ba su tsaro.Trump ya bayyana haka ne a yayin ziyarar ba-zata da ya kai wa dakarun Amurka da ke Iraqi, kuma ya bayar da tabbacin cewa, ba zai janye dakarun ba kamar yadda ya yi a Syria. Sai dai tuni masharhanta kan al’amuran siyasa suka alakanta ziyarar Trump da wani yunkurin wanke kanshi daga caccakar da ake yi masa a ciki da wajen kasar, kamar yadda za ku ji karin bayani a hirar da Abdurrahman Gambo ya yi da Alh. Sulaiman Garba Krako Saminaka da ke fashin bakin siyasa a Amurka.

Shugaban Amurka Donald Trump tare da maidakinsa Melania Trump yayin ziyarar bazata da ya kai wa dakarunsa da ke yaki a Iraqi.
Shugaban Amurka Donald Trump tare da maidakinsa Melania Trump yayin ziyarar bazata da ya kai wa dakarunsa da ke yaki a Iraqi. 路透社。
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.