Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Shugaban Ukraine ya gana da iyalan matukan jirgin da Rasha ke tsare da shi

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya sanar iyalan matukan jirgin ruwan da Rasha ta kama ta tsare cewar zai yi iya bakin kokarin sa wajen dawo da su gida.

Wasu jiragen ruwan yaki na kasar Ukraine
Wasu jiragen ruwan yaki na kasar Ukraine REUTERS / Alla Dmitrieva
Talla

Kasashen Ukraine da Rasha sun dukufa wajen lalibo hanyoyin warware takaddamar tsawon shekaru a tsakaninsu, inda mahukunta a Kiev da abokan kawancensu na kasashen yammaci, suka bukaci Rasha da ta sallami jirgin ruwan ukrain da jami’an tsaron gabar ruwanta suka kama a kan ruwan yankin Crimea da ke karkashin ikon Rasha.

A cewar kakakin fadar Kremlin na Rasha Dmitri Peskov, Rasha ta kare matsayinta da cewa, ta yi haka ne a karkashin dokokin duniya, bayan da ta zargi jirgin ruwan na Ukraine da shiga farfajiyar Ruwan kasar ta.

Yayin ganawa da iyalan, shugaban yace abinda ke gaban sa shine ganin matukan sun dawo gida, yayin da yake cewa gaba daya al’ummar kasar Ukraine na alfahari da su.

Tuni wata kotu a Rasha ta bada umurnin cigaba da tsare matukan jirgin da aka kama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.