Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Amurka ta bukaci kakabawa Iran sabbin takunkumai

Amurka ta bukaci kasashen Turai su kakaba wa Iran sabbin takunkumai saboda har yanzu Iran na ci gaba da kasancewa barazana ga tsaron duniya ta hanyar kera makamai masu cin dogon zango.

Sabon makami mai linzami da kasar Iran ta kera, yayin gwajinsa a wani yankin kasar. 11/10/2015.
Sabon makami mai linzami da kasar Iran ta kera, yayin gwajinsa a wani yankin kasar. 11/10/2015. REUTERS/farsnews.com
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana haka, a lokacin da yake sukar matakin Iran na gwajin wani makami mai linzami da ta kera mai cin matsakaicin zango a karshen mako, wanda zai iya dakon makamai masu guba, zuwa sassan nahiyar Turai da kuma baki dayan yankin Gabas ta Tsakiya.

Pompoe ya ce kera irin wadannan makamai, abu ne da ya yi hannun riga da kudurin Mjalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 da ya bukaci takaita irin makaman da kasar ke kerawa.

Bayaga Amurka, ma’aikatar harkokin wajen Faransa ma ta yi soki gwajin makamin na Iran, wanda ta bayyana shi a matsayin tsokanar da ka iya tayarda zaune tsaye.

A watan Mayu na wannan shekara, Amurka ta fice daga cikin yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya a shekarar 2015, tare da maida takunkuman da Amurkan ta cirewa Iran a zamanin mulkin Barack Obama.

Amurka ta dauki matakin ne domin tilasta sake fasalin yarjejeniyar nukliyar, wadda ta ce bata takaita yawan kera manyan makamai masu linzami da Iran din ke yi ba, da kuma takaita tasirinta a harkokin tsaro da Diflomasiyya na yankin Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.