Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Trump zai gana da XI da Putin don dakile kera muggan makamai

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci ganawa da takwarorinsa na Rasha da China don tattaunawa da nufin kawo karshen yawan kera muggan makaman da kasashen ke rige-rigen samarwa.Trump wanda ya kira shirin kera muggan makaman na manyan kasashe da gasa, ya ce abin takaici ne irin kudaden da ake kashewa bangaren kowacce shekara.

Makamai masu Linzami.
Makamai masu Linzami. static4.depositphotos.com
Talla

A wani sakon Twitter da ya wallafa Donald Trump ya ce akwai yiwuwar ganawar tsakaninsa da Vladimir Putin na Rasha da Xi Jinping na China don tattauna yadda za a dakile matsalar kera muggan makamai da manyan kasashe ke yi.

Shugaban na Amurka Donald Trump, ya ce abin takaici ne yadda Amurka ta kashewa bangaren kera muggan makamai tsabar kudi har dala biliyan 716 a bana, matakin da ya ce akwai yiwuwar ganawarsa da manyan kasashen wadanda suka kai makura wajen kera makamantan makaman don yi wa tufkar hanci.

Sanarwar ta Trump na zuwa ne kasa da watanni 2 bayan da ya yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar kera manyan makamai da ke tsakaninsa da Rasha, batun da ya tayar da hankali wanda kuma ke barazana ga tsaron duniya, la’akari da yadda kasashen za su ci gaba da kera makamai ba waigi.

A baya dai Trump ya sha alwashin bunkasa sashen makamai na Amurka dalilin da yasa ya yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar wadda aka cimma tun a shekarar 1987 ba kuma tare da sanyo China a ciki ba, ko da dai ana ganin tsamin alakar Amurkan da Rasha ya zama wajibi ya sanyo China kan batun don samar da daidaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.