Matakin na zuwa ne bayan Amurka ta kaddamar da shirin tattaunawa da kungiyar Taliban bayan kwashe shekaru 17 ta na yaki da ita ba tare da samun galaba ba.
Ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta ce a wasikar, shugaba Trump ya bayyana sasanta rikicin Afghansitan a matsayin mafi muhimmanci a gare shi a Yankin, saboda haka yana bukatar taimakon Pakistan.
Paksitan ta dade ta na nesanta kan ta da 'yan kungiyar Taliban.