Isa ga babban shafi
Afghanistan-Majalisar Dinkin Duniya

UNICEF ta koka da matakin daukar yara mata kadara a Afghanistan

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce, iyaye na sayar da ‘ya’yansu mata ta hanyar aurar da su ga masu hali don samun kudin da za su biya bashi da shi ko kuma sayen abinci a Afghanistan mai fama da matsalar fari da sauran rikice-rikice.

FILE PHOTO: Newly displaced Syrian children arrive at a refugee camp in Atimah village, Idlib province, Syria September 11, 2018.
FILE PHOTO: Newly displaced Syrian children arrive at a refugee camp in Atimah village, Idlib province, Syria September 11, 2018. REUTERS/ Khalil Ashawi/File Photo
Talla

Asusun na UNICEF ya kiyasta cewa, akalla kananan yara 161 da shekarunsu ya kama daga wata guda zuwa shekara 16, aka sayar a cikin watanni hudu da suka shude a lardunan Herat da Baghdis da ke fama da mummuar matsalar pari a Afghanistan.

Mai magana da yawun UNICEF, Alison Parker ta shaida wa manema labarai cewa, halin da yaran ke ciki ya tsananta a kasar ta Afghanistan.

Parker da ke magana a dai dai lokacin da ake gudanar da wani taron tattaunawa kan Afghanistan a birnin Swiss, ta ce, bincikensu na watan Yuli zuwa Oktoba, ya nuna cewa, ko dai an yi wa yaran mata baiko ko kuma yi musu auren dole saboda matsalar bashin da ta dabaibaye iyayensu.

A cewar Parker, kashi 80 cikin 100 na iyaye a Afghanistan, sun tsindima cikin bashi tun gabanin ibtila’in pari a kasar bayan akasarinsu sun dogara da albarkatun gona don samun abin da za su biya bashin da shi, amma hakan ya ci tura saboda parin.

Yanzu haka dai, ana daukan yara mata tamkar kadara a Afghanistan, al’marin da Majalisar Dinkin Duniya ta koka da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.