Isa ga babban shafi
Amurka-Saudi

CIA ba ta sanar da hannun bin Salman a kisan Khashoggi ba- Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta rahotanni da ke cewa hukumar tsaron kasar ta CIA ta tabbatar da cewa Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad Bin Salman ne ya yi umarnin kisan Dan jarida Jamal Khashoggi a birnin Santambul na Turkiya ranar 2 ga watan Oktoba.

Yanzu haka dai Muhammad bin Salman na ziyara a hadaddiyar daular Larabawa wadda tuni ya samu tarbe daga yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Muhammad bin Zayed.
Yanzu haka dai Muhammad bin Salman na ziyara a hadaddiyar daular Larabawa wadda tuni ya samu tarbe daga yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Muhammad bin Zayed. REUTERS/Amir Levy/File Photo
Talla

Kalaman na Trump na zuwa a dai dai lokacin da Muhammad bin Salman ke ziyara karon farko zuwa wata kasa tun bayan kisan na Khashoggi da ya sanya Saudiyyar fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya da ma kungiyoyin kare hakkin dan adam.

A cewar Trump kawo yanzu CIA na tantama ne kan ko akwai hannun Yariman a kisan inda ta nemi amincewarsa don gudanar da bincike amma mahukuntan kasar suka yi watsi da batun.

Da ya ke amsa tambayar manema labarai a Florida, shugaban na Amurka Donald Trump ya nanata cewa CIA ba ta ambaci Yariman na Saudiya a rahoton ta ba, yana mai cewa sai dai idan akwai wadanda ke son kara sunansa cikin mutane 18 da ake zargi da kisan.

Yanzu haka dai Muhammad bin Salman na ziyara a hadaddiyar daular Larabawa wadda tuni ya samu tarbe daga yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Muhammad bin Zayed.

Ka zalika bin Salman wanda ke shirye shiryen halartar taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki da zai gudana a Buenos Aires karshen watan nan, a can zai gana da Recep Tayyib Erdogan na Turkiya wanda ke ci gaba da nanata cewa lallai umarnin kisan Khashoggi ya zo ne daga babban Ofishi na Saudiyan ko da dai kai tsaye bai ambaci sunan Yariman ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.