Isa ga babban shafi
Yemen

Za a sasanta rikicin Yemen a cikin watan Disamba- Amurka

Amurka ta ce, za a gudanar da tattaunawar kawo karshen rikicin Yemen a farkon watan Disamba mai zuwa a Sweden, in da ‘yan tawayen Houthi da bangaren gwamnati da kuma hadakar dakarun da Saudiya ke jagoranta za su halraci zaman.

Wani barin wuta a tashar jirgin Hodeidah da ke Yemen
Wani barin wuta a tashar jirgin Hodeidah da ke Yemen AFP
Talla

Sakataren Tsaron Amurka, Jim Mattis ya ce, Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da ke goyon bayan shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi a mummunan rikicin tsawon shekaru uku, sun shirya halartar zaman sulhun.

Kalaman Mattis na zuwa ne a dai daai lokacin da manzan musamman na Majalisar Dinkin Dunya, Martin Griffith ya isa birnin Sanaa don ganawa da ‘yan tawayen da zummar shawo kansu don shiga cikin tattaunawar sulhun a Sweden.

Mayakan Houthi sun ki halartar taron zaman lafiyar da aka shirya a Switzerland a cikin watan Satumba, lamarin da ya yi sanadiyar tabarbarewar wancan yunkuri na warware rikicin kasar da ya lakume dubban rayuka.

Mayakan sun ce, suna bukatar kasashen duniya su ba su tabbacin kare lafiyarsu don ganin sun wuce ba tare da wata fargabar farmaki ba daga rundunar hadakar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla mutane miliyan 14 na cikin barazanar kamuwa da yunwa a Yemen muddin tashin hankalin ya kai ga rufe tashar jirgin ruwa ta birnin Hideida, wato hanyar da kungiyoyin agaji ke amfani da ita wajen isar da kayayyakin agaji ga al’ummar Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.