Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na cacar baka da shugaban kotun kolin Amurka

Shugaban Kotun Kolin Amurka, John Roberts ya caccaki shugaban Amurka Donald Trump game da kalaman da ya furta kan wani alkalin kotun tarayya, Jon Tigar da ya yi watsi da shirinsa na hana ‘yan gudun hijira mafaka a kasar.

Shugaban Amurka Donald Trump  da shugaban alkalin kotun kolin kasar John Roberts
Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban alkalin kotun kolin kasar John Roberts REUTERS/Jonathan Ernst/File Photo
Talla

A ranar Talatar da ta gabata ne, Mr. Trump ya bayyana alkalin kotun tarayyar a matsayin “Alkalin Obama” bayan ya soke umarninsa na hana ‘yan gudun hijirar mafaka.

Kalaman Trump sun harzuka shugaban kotun kolin wanda a karon farko kenan da yake sukar Trump duk da cewa, mawuyacin al’amari a samu sa-in-sa tsakanin wani baban alkali da wani shugaban Amurka

A yayin mayar da martini, Mr. Roberts ya ce, “ ba su da alkalan Obama ko alkalan Trump ko alkalan Bush ko kuma alakan Clinton, in da yake cewa, kungiyarsu ta kunshi zaratan alkalai da ke aiki tukuru wajen tabbatar da ‘yancin mutanen da ke shigar da kara a gabansu.

Sai dai tuni shugaba Trump ya mayar da martani a shafinsa na Twitter, in da ya ce, shugaban kotun kolin ya yi kuskukure kuma ya nanata cewa, “alkalan Obama” na da wani ra’ayi na daban idan aka kwatanta su da wadanda alhakin tabbatar da zaman lafiyar Amurka ya rataya a wuyansu.

Trump na ganin cewa, matakin alkalin na dakatar da umarninsa, ya yi hannun riga da shirinsa na kare kan iyakar kasar daga kwararar bakin ‘yan gudun hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.