Isa ga babban shafi
MDD-Myanmar

Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi Bangladesh kan mayar da 'yan Rohingya

Shugaban Hukumar Kare Hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci kasar Bangladesh da ta dakatar da shirinta na fara dawo da 'yan gudun hijirar Rohingya zuwa kasar su Myanmar, inda ya yi gargadin cewa, yin hakan sake tsananta take hakkokin tsirarun kabilar Musulmai ne.

yan gudun hijirar rohingyas na ketara kogin Naf domin isa Bangladesh, a ranar 12 novemba 2017
yan gudun hijirar rohingyas na ketara kogin Naf domin isa Bangladesh, a ranar 12 novemba 2017 REUTERS/Mohammad Ponir Hossain
Talla

Hukumomin Bangladesh sun ce, daga ranar alhamis ne zasu fara kwashe ‘yan gudun hijirar ‘yan kabilar Rohigya, zuwa kasar su domin sake hadasu da takwarorinsu na Buda da suka tserewa tun farko, sakamakon kisan kare dangi da ake musu, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira shafe tsirarun musulman ne kawai.

Matakin da tuni ya haifar da tsoro a sansanonin, inda ya sa wasu iyalan gudu, masamman wadanda aka bayyana sunayensu cikin rukunin farko na wadanda za’a fara komawa da su gida.

Cikin wata sanarwa, babban kwamishinan kare hakkin dam’adam a Majalisar Dinkin Duniya, Michelle Bachelet, ya ce yanzu haka suna samun rahotanni daga kasar Myanmar da ke nuna cewa, ana ci gaba da cin zarafin ‘yan kabilar ta Rohingya a can, don haka, ya kira hukumomin Dhaka da suyi la’akari da wannan.

Bachelet ya ce, tilastawa masu neman mafaka komawa gida, na amatsayin take hakkokin su ne da kuma yancin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.