Trump ya kori Ministan Shari'ar Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump ya kori Ministan Shari’arsa Jeff Sessions, kwana guda da gudanar da zaben tsakiyar wa’adi, in da jam’iyyar Republican mai mulki ta rasa rinjaye a zauren Majalisar Wakilai.
Wallafawa ranar:
A wani sakon Twitter da ya aika, shugaba Trump ya mika godiya ga Sessions kan gudunmawar da ya bayar tare da yi masa fatan alheri.
Shugaba Trump ya sha caccakar tsohon Ministan Shari’ar bayan ya tsame kansa daga binciken da ake gudanarwa kan zargin Rasha da yin katsalandan a zaben Amurka na 2016.
Trump ya ce, shugaban ma’aikata a ofishin Sessions, Mathew Whitaker wanda ya sha sukar binciken kutsan Rashan, zai maye gurbin Ministan Shari’a na rikon kwarya.
Ana ganin wannan matakin na Trump zai kara janyo cece-kuce game da makomar binciken kutsan zaben, in da wasu ke zargin cewa, fadar White House na kokarin kashe maganar binciken ne baki daya.
A bangare guda, ana hasashen cewa, akwai yiwuwar Trump ya yi garambawul a Majalisar Ministocinsa bayan kammala zaben na tsakiyar wa’adi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu