Sama da ‘yan Rohingya dubu 700 yanzu haka ke samun mafaka a Bangladesh bayan da suka gujewa cin zarafin da jam’ian tsaron kasar Myanmar ke yi masu.
Myanmar da Bangladesh sun amince zuwa 30 ga watan daya gabata za’a mayar da masu gudun hijiran, amma kuma mai binciken ta MDD na ganin an yi gaggawa.
A ranar larabar da ta gabata ne ne 31 ga watan Octoban da ya gabata wani babban jami’an gwamnatin Bama ya tabbatar da sake komawar kimanin yan kabilar Rohingya dubu 2000 gida daga sansanin yan gudun hijira dake kasar Bangladesh.