Isa ga babban shafi
Farans- Duniya

An fara bikin cika shekaru 100 da yakin duniya na farko

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kaddamar da bukukuwan cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na farko, in da ya gargadi yaduwar matsalar tsananin kishin kasa da ta zama ruwan dare a sassan duniya.

Rundunar Sojin Jamus a birnin Paris a lokacin yakin duniya
Rundunar Sojin Jamus a birnin Paris a lokacin yakin duniya Folkerts, Bundesarchiv
Talla

Ana saran kimanin shugabannin kasashen duniya 70-80 da suka hada da na Amurka, Donald Trump da na Rasha Vladimir Putin su halarci bukukuwan a birnin Paris na Faransa.

Tuni shugaba Macron ya fara zagaye sassan Faransa, in da zai ziyarci yankunan da aka gwabza yakin na duniya a yammaci da gabashin kasar.

Macon zai kuma yi amfani da damar wannan bikin wajen gabatar da kokensa kan matsalar tsananin kishin kasa, lura da cewa, a kwanan nan ne ya gargadi cewa, kasashen duniya na neman mancewa da darussan tashe-tashen hankulan da aka gani a karni na 20.

Shugaban ya ce, ya damu da yanayin da ake rayuwa a yanzu idan aka kwatanta da zamanin yake-yaken duniya na farko da na biyu, kuma a cewarsa matsalar ta kishin kasa tamkar kuturta ce da ke yaduwa a duniya.

Shugaba Trump da ke cewa, manufar Amurka ce a gaba da komai, na cikin mayan bakin da za su halarci gagarumin bikin a Arc de Triomphe a Paris.

Bikin na tsawon mako guda, zai kai ga shugabannin ga halartar kushewar wani jarumin soja a Champs Elysee a cikin tsauraran matakan tsaro musamman ganin munanan hare-haren ta’addancin da ISIS ta kai wa Faransa a shekarun da suka gabata.

A jiya Lahadi, an gudanar da kade-kade da raye-rayen zumunci tsakanain Faransa da Jamus da suka kasance manyan abokan gaba da juna a lokcin yakin duniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.