Isa ga babban shafi
Turkiya-Saudiya

Wani kusa ne a gwamnatin Saudi ya yi umarnin kisan Khashoggi- Erdogan

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce yana da yakinin cewa an bayar da umarnin kisan Fitaccen dan jaridar Saudiyya Jamal Khasgohhi ne daga babban Ofishin gwamnatin Saudin a Riyadh ba wai kai tsaye mutanen da ake zargin suka aikata kisan ba.

Akwai dai zarge-zarge da ke ganin da hannun Yarima mai jiran gado na Saudiyya a kisan na Khashoggi wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar gidan sarautar.
Akwai dai zarge-zarge da ke ganin da hannun Yarima mai jiran gado na Saudiyya a kisan na Khashoggi wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar gidan sarautar. REUTERS/Tumay Berkin
Talla

Cikin kalaman shugaban Turkiyyan na baya-bayan nan game da kisan Khashoggi ya ce dole ne wani babban kusa a gwamnatin Saudin ne ya yi umarnin kisan amma ba zai taba zama Sarki Salman ba.

A cewar Erdogan ko kadan dai dai da dakika daya ba zai taba amincewa Sarki Salman ne ya yi umarnin kisan ba, haka zalika bashi da masaniya a batun, amma dai tabbas wani na jikinsa ne da ke da ikon fada aji a mulkin kasar.

Akwai dai zarge-zarge da ke ganin da hannun Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman a kisan na Khashoggi wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar gidan sarautar, ko da dai manyan jami'an gwamnatin kasar na ci gaba da nanata cewa babu hannun yariman na su a ciki.

Haka zalika shi da kansa Yarima Muhammad Bin Salman ya fito karara ya bayyana cewa basu da masaniya kan wadanda ke da hannu a kisan na Khashoggi yayinda ya sha alwashin gudanar da bincike.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.