Farfesa Umar Pate kan ranar yaki da gallazawa 'Yan Jaridu
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:56
Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar yaki da gallazawa Yan Jaridu ta duniya, wanda ake amfani da ita wajen fadakar da jama’a kan muhimmancin aikin Jarida da kuma mutunta ma’aikatan.Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, a sakon da ya aike a wannan ranar, ya bayyana takaicin sa kan yadda ake kaiwa Yan Jaridu hari, inda yake cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata, Yan Jaridu 1,010 aka kashe, kuma har ya zuwa yau ba’a hukunta kashi 90 na wadanda suka aikata kisan ba.Dangane da wannan rana, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Prof Umar Pate na Jami’ar Bayero, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.