Isa ga babban shafi
Amurka-Mexico

Trump zai zaftare tallafin kasashen tsakiyar Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, zai fara zaftare tallafin da kasar ke bai wa Guatemala da Honduras da El Salvador sakamakon yadda ayarin dubban ‘yan gudun hijirar kasashen ke dosar kan iyakar Amurka.

Ayarin 'yan gudun hijirar da ya doshi Amurka
Ayarin 'yan gudun hijirar da ya doshi Amurka REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Akasarin wadandan mutane sun fito ne daga Honduras, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa, yanzu haka sama da mutane dubu 7 ne suka doshi Amurka kuma wasu ‘yan gudun hijirar daban sun hade da su.

Shugaba Donald Trump ya ce, tuni ya sanar da jami’an tsaron kan iyakokin Amurka game da wannan gagarumin ayari da ya bayyana a matsayin dokar ta baci.

Shugaban ya kuma ce, nan kusa za su fara rage tallafin da suke bai wa kasashen na yankin tsakiyar Amurka.

Hukumomin Mexico sun yi kokarin kange wasu ‘yan gudun hijira akan kan iyakar kasar da Guatemala bayan sun kwarara ta shingayen Guatemala a ranar Juma'ar da ta gabata, amma duk da haka sai da ‘yan gudun hijirar suka ratsa ta kwale-kwalen roba.

Wannan ayarin ya ci gaba da tattakinsa a jiya Litinin a jihar Chiapas da ke kudancin Mexico.

Shugaba Trump ya ce, abin takaici ne yadda jami’an tsaron Mexico da suka hada da sojoji suka gaza dakile ayarin da ya doshi Amurka.

Trump ya ce, akwai miyagu da wasu ‘yan yankin gabas ta tsakiya da suka hade da wannan ayari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.