Isa ga babban shafi
Saudiya-Turai

Jamus na son nahiyar Turai ta yanke hulda da Saudiya

Jamus ta bukaci kasashen Turai da su hada kai wajen dakatar da dukkanin wata alakar kasuwanci tsakaninsu da Saudiya da ta kunshi yarjejeniyar sayar ma ta da  makamai, biyo bayan zargin gwamnatin Saudiya da hannu cikin mutuwar dan Jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancinta da ke birnin Santanbul.

Ana zargin yarima mai jiran gado da hannu a mutuwar Khashoggi
Ana zargin yarima mai jiran gado da hannu a mutuwar Khashoggi BANDAR AL-JALOUD / Saudi Royal Palace
Talla

Yayin da yake jadadda bukatar kakaba wa Saudiya takunkumin cinikin makaman, Ministan Lura da Tattalin Arzikin Jamus Peter Altmaier ya ce, tilas ne ilahirin kasashen Turai su hada kai kan kudurin, muddin ana bukatar ganin tasirin daukar matakin ladabtarwar.

A gefe guda, kakakin shugabar gwamnatin Jamus, Steffen Seibert ya ce, suna tattaunawa kan yiwuwar soke cinikin makaman da suka riga suka kulla da Saudiya a baya-bayan nan.

A watan Satumban da ya gabata, Jamus ta amince da saida wa Saudiya makaman da darajarsu ta kai Euro miliyan 416, sai dai kawo yanzu bata kai ga mika mata su ba.

Bayan shafe kwanaki ta na musanta masaniyar halin da Khashoggi ke ciki, a ranar Asabar, Saudiya ta amsa cewa babu tantama an kashe dan jaridar a ofishin jakadancinta da ke birnin Santanbul na Turkiya, bayan ya shiga ofishin a ranar 2 ga watan Oktoban da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.