Isa ga babban shafi
MDD

"Ya kamata a kawo karshen gwajin budurcin 'ya mace"

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci haramta gudanar da gwajin budurcin ‘ya mace don sanin ko ta yi lalata da wani Da namiji, abin da hukumomin suka bayyana matsayin keta hakkokin mata.

Kimanin kasashen duniya 20 na gudanar da al'adar yi wa mace gwajin budurci kafin aurenta.
Kimanin kasashen duniya 20 na gudanar da al'adar yi wa mace gwajin budurci kafin aurenta. Getty Images/Aldo Pavan
Talla

Hukumomin sun bayyana haka ne a taron tattaunawa kan matsalolin da suka shafi mata da suka hada da batun haihuwa da ke gudana a birnin Rio de Janeiro.

Hukumomin da suka fitar da sanarwar sun hada da Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Kare Hakkokin Mata da kuma Hukumar Lafiya ta duniya.

Da dama daga cikin kasashen Afrika na gudanar da irin wannan gwajin budurcin mace, in da ake cusa ‘yan ‘yatsu a cikin tsaraicinta da zummar sanin ko ta kawar da budurcinta ta hanyar lalata da wani.

Hukumomin sun ce, wannan al’amari ba shi da amfani a likitance kuma yana haifar da radadi ga ‘ya mace tare da kaskanta ta.

Mafi tarin lokuta ana yi wa mata wannan gwajin ne gabanin bikin aurenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.