Isa ga babban shafi
Rasha-Crimea

Dalibai 13 sun mutu a harin ta'addancin yankin Crimea

Akalla dalibai 13 suka mutu yayinda wasu 50 kuma suka jikkata yau a wata kwalejin kimiyya da Fasaha da ke birnin Kerch a Crimea sakamakon wata fashewa a dakunan cin abincin makarantar.Tuni dai gwamnatin Rasha ta bayyana fashewar da yunkurin harin ta’addanci yayinda ta sha alwashin fara bincike.

Jami'an agaji lokacin da su ke aikin kai dauki ga wadanda suka jikkata a harin na kwalejin kimiyya da Fasaha ta birnin Kerch a yankin Crimea.
Jami'an agaji lokacin da su ke aikin kai dauki ga wadanda suka jikkata a harin na kwalejin kimiyya da Fasaha ta birnin Kerch a yankin Crimea. Fuente: Reuters.
Talla

Fashewar wadda ta faru da misalin karfe 12 na tsakar ranar yau, rahotanni sun ce galibin wadanda suka mutu dalibai ne matasa da shekarunsu bai gaza 14 ba.

Wasu ganau sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a dai dai lokacin da daliban ke tsaka da cin abinci a kebantaccen ginin da makarantar ta ware musu.

Wata tashar talabaijin a yankin ta nuna yadda motocin agaji suka rika sintiri a makarantar don bayar da taimakon gaggawa ga daliban da suka jikkata, haka zalika sashen bayar da agajin gaggawa na yankin ya aike da jiragen shalkwafta don kwashe wadanda suka samu rauni.

Tuni dai shugaba Vladimir Putin ya aike da sakon jaje ga iyalan wadanda abin ya shafa, yayinda jagoran yankin Sergei Aksyonov ya ce sun dauki dukkan matakan da suka da ce don agazawa wadanda harin ya rutsa da su.

A bangare guda kuma kwamitin da gwamnatin Rasha ta kafa don bincikar yiwuwar ta’addanci a fashewar ya sha alwashin lalubo wadanda ke da hannu a harin na birnin Kerch da ke yankin Crimea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.