Isa ga babban shafi
Tattalin Arziki

Duniya na tafka hasarar sama da dala bilyan 133 na cinikin mai

Wani rahoton bincike ya tabbatar da cewa a kowace shekara ana tafka hasarar sama da dalar Amurka bilyan 133 sakamakon cinikin gurbataccen man fetur a kasuwannin bayan fage da ke sassan duniya.

Kudaden cinikin danyen mai a duniya sama da dala biliyan 133 na zurarewa ta kasuwannin bayan fage.
Kudaden cinikin danyen mai a duniya sama da dala biliyan 133 na zurarewa ta kasuwannin bayan fage. REUTERS/Alkis Konstantinidis
Talla

Wannan dai sakamakon wani bincike ne da jami’ar Yale da ke kasar Amurka ta gudanar, wanda ke nuni da cewa kungiyoyin da ke aikata miyagun laifufuka da suka hada da IS, Boko Haram, ‘yan Mafia a kasar Italiya da sauran kungiyoyi da ke kasar Mexico ne ke amfana da kudaden.

An kiyasta cewa a kowace shekara kasuwar man fetur na samar wa kasashen duniya kudaden da yawansu ya kai dala Tiriliyan daya da bilyan 700, to amma sama da bilyan 133 na fadawa ne a hannun kungiyoyi masu aikata miyagun laifufuka.

Kasashen Libya, Najeriya, Iraki Mexico da kuma Rasha ne suka fi yin asara sakamakon yadda ake sace gurbataccen man sannan a sayar da shi a cikin kasuwanni musamman a Yankin Turai da kasashen kudancin Amurka.

A cewar rahoton, Najeriya kawai, tana tafka hasarar sama da dala bilyan 17 a kowace shekara sakamakon yadda ake fasa bututu da kuma barayi da ke karkata akalar gurbataccen mai mallakin kasar.

Kashi 9% na man da ake amfani da shi a Italiya na sata ne a cewar rahoton, yayin da adadinsa zai kai 20% a kasar Girka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.