INVITE- WORLD FOOD DAY IS TODAYYau ne ranar da Majalisar Dinkin Duniya a matsayin ranar abinci ta Duniya, in da masana ayyukan da suka shafi noma da abinci ke muhawara game da in da aka kwana a kokarin wadata jama’a da abincin da suke bukata. Garba Aliyu Zaria ya nemi ji daga bakin Sarkin Noman Najeriya, Alhaji Muhammadu Hakimi Jiga wanda kuma shi ne Sarkin Noman jihar Kebbi, ko manoman kasar sun noma wadataccen kayan abinci da jama'a za su ci har su tuna wannan rana?
Sauran kashi-kashi
-
Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike
Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba.18/04/202403:16 -
Kuskure ne a yi tunanin ɗagawar darajar naira ba zai ɗore ba - Dakta Kurfi
Darajar Naira na cigaba da ɗagawa a Najeriya tare da saukar farashin wasu kayayyakin abinci a wasu kasuwannin ƙasar, abinda ya sa wasu tunanin cewar tasirin saukar Dalar ne ya sanya wasu kayayyakin suka fara sauka.17/04/202403:19 -
Tattaunawa da Sanata Ikira Aliyu Bilbis kan tsaro a jihar Zamfara
Hukumomi a Najeriya daga matakin jiha zuwa na kasar baki ɗaya na daukar matakai daban daban wajen samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, amma har ya zuwa wannan lokaci ba'a kai ga cimma biyan bukata ba.16/04/202403:26 -
Yadda rayuwa ta kasance bayan da muka faɗa hannun mayakan Boko Haram - Maryama
A ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilun nan aka cika shekaru 10 da sace dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok sama da 250 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno.15/04/202403:17 -
Kwamred Bello Basi kan shirin gina hanyayoin zamani a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sanar da kashe naira biliyan 4 kan kowacce kilomita ta hanyar zamani da ake ginawa daga jihar Legas zuwa birnin Kalaba.12/04/202403:40