Isa ga babban shafi
FAO-Duniya

Tilas gudun hijira ya zama zabi ba dole ba - FAO

Hukumar samar da abinci da ayyukan gona ta majalisar dinkin duniya, FAO, ta kaddamar da tarukan sharar fage, kan bikin ranar abinci ta duniya wanda Italiya ke karbar bakunci.

Wani yanki na kasar Sudan ta Kudu dake fama da matsalar karancin abinci.
Wani yanki na kasar Sudan ta Kudu dake fama da matsalar karancin abinci. REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Bikin dai na gudana ne a kowace irin rana ta gobe, wato 16 ga watan Oktoba, domin nazarin matsalolin da ke addabar kokarin samar da abinci a duniya.

Bisa al’ada, bikin wanda aka kaddamar a wannan Litinin, za’a shafe mako guda ne ana gudanar da shi, domin tattaunawa kan matsalolin da suka yiwa burin wadatar abinci a duniya dabaibaiyi, da kuma tunawa da shekarar 1945, lokacin da aka kafa hukumar samar da abincin da ayyukan gonar ta FAO.

Bikin wannan shekarar ya soma da wallafa rahoto kan alakar matsala ta yawaitar gudun hijira, da wadatar abinci, bunkasar ayyukan noma da kuma yawaitar yadda mazauna karkara ke yin kaura zuwa birane a kasashen duniya.

Sabon rahoton na hukumar ta FAO, ya ce, duk shekara, akalla mutane biliyan daya dake rayuwa a kasashe masu tasowa ke yin gudun hijira a cikin kasashen nasu, a dalilin karancin abinci, da durkushewar ayyukan gona saboda tashe tashen hankula da sauyin yanayi, matsalar da rahoton yace ta girmama, fiye da matsalar kwarar bakin-haure daga wata kasa zuwa wata.

Taken bikin ranar abincin ta duniya a wannan shekara dai shi ne, “Ya zama dole batun gudun hijira ya zama abu ne na zabi ba tilas ba”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.